Barazana ga zaman lafiya a cikin kasashen duniya ita ce ta'addanci. Duk wasu matakan tsaro da duk wasu dabarun yaki ya kamata a tanade su, in ji mista Tsaty-Mabiala a yayin bikin bude zaman taron musammun na kwamitin kasa na jam'iyyar UPADS.
Babbar matsalar, ita ce barazanar ta'addanci dake bazuwa a yankin Sahel a halin yanzu tare da tsirarrun kungiyoyin ta'addanci kamar AQMI da Ansar-Dine da sauransu.
A cewar mista Tsaty-Mabiala, kasar Congo, dake iyaka da Kamaru da Afrika ta Tsakiya, ba za ta tsira ba har nan zuwa wani lokaci kuma dole ta nuna damuwa.
Kusa da kan iyakokin wasu kasashen Afirka, kungiyar Boko Haram na gudanar da ayyukan ta'addanci a kasashen Najeriya, Chadi, Nijar da Kamaru, tare da nuna cewa ci gaban da kungiyar IS take samu na kokarin kafa daular kasar musulunci na zama bazarana ga zaman lafiya a duniya. (Maman Ada)