in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
RD-Congo: Masu rinjaye da masu adawa sun samu rarrabuwar kawuna kan matsayin da MONUSO a lokacin zabe
2016-04-01 10:24:59 cri
Bangaren adawa na jamhuriyar dimokuradiyyar Congo ya kira a ranar Alhamis ga MDD da ta karfafa tallafin kayayyakin da take bayar domin shirya zabuka a cikin wa'adin kundin tsarin mulki, a lokacin da masu rinjaye dake mulki suka nuna cewa gudanar da zabuka ba ya dogaro da MDD, amma da yanayin da kasa take ciki.

Sakatare na jam'iyyar MLC, madam Eve Bazaiba Masudi, ta yi kiran MDD da ta karfafa tallafin kayayyakin tawagar MONUSCO domin gudanar da zabuka bisa wa'adin kundin tsarin mulki.

A nasa bangare, kakakin masu rinjaye dake mulki (MP), Andre-Alain Atundu, ya bayyana cewa gudanar da zabuka yana da nasaba, ba kawai da kudurorin MDD, amma da halin aikin hukumar zabe mai zaman kanta (CENI) da kuma fahimtar da aka cimma tsakanin jam'iyyun siyasar kasar Congo.

Mutanen biyu sun yi furucin a ranar Alhamis a gidan rediyon MDD, a jajibirin amincewa da kudurin kwamitin tsaro ma MDD na kara wa'adin aikin tawagar wanzar da zaman lafiya ta MDD dake RD-Congo (MONUSCO) da shekara guda tare da yin kira da a gaggauta gudanar da zabuka cikin 'yanci ba tare da magudi ba.

'Yan adawa dai na zargin shugaba Joseph Kabila, dake kan karagar mulki tun a shekarar 2001, da neman kaucewa haramcin kundin tsarin mulki dake hana shi neman wa'adin mulki na uku. A nasa bangare mista Kabila ya kaddamar da wani zaman taron sasanta 'yan kasa domin shirya zabuka cikin kwanciyar hankali ba tare da wani magudi ba. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China