in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta kara wa'adin shekara guda na tawagarta da ke RD-Congo
2016-03-31 10:48:05 cri
Kwamitin sulhu na MDD ya cimma a ranar Laraba da wani kudurin kara wa'adin tawagar wanzar da zaman lafiya ta MDD da ke jamhuriyyar demokaradiyar Congo ( MONUSCO) har zuwa ranar 31 ga watan Maris din shekarar 2017.

Kwamitin sulhun zai rike adadin dakarun MONUSCO kimanin dubu 20 tare da jaddada cewa tsare tsaren tawagar zasu gudana ta la'akari da cigaban da ake samu wajen tafiyar da muhimman ayyukan, kamar kare fararen hula da daidaita al'amura.

MONUSCO ta yi kiran samar da taimakon kwarewa da tallafin kayan aiki domin kawo gyara kan takardun zabe domin tabbatar da ganin an gudanar da zabuka, wannan tallafin za'a cigaba da kiyasta shi bisa la'akari da cigaban da aka samu daga hukumomin kasar Congo wajen tafiyar da ayyukan zabuka.

Kwamitin ya bukaci, hukumar zabe mai zaman kanta da ta gabatar da jadawalin zaben karshe da aka yi wa gyaran fuska da ke kunshe da dukkan tanade tanaden zabe, tare da yin kira ga gwamnatin RDC da ta tsara wani kasafin kudi cikin gaggawa da kundin zabe domin sabunta takardun zabe bisa gaskiya domin gudanar da zabuka cikin lokaci, musamman zaben shugaban kasa da na majalisar dokoki a cikin watan Nuwamban shekarar 2016.

Haka zalika, kwamitin ya yi kira ga bangarori masu ruwa da tsaki da su himmatu wajen fara shawarwain siyasa bisa aldaci da gaskiya kan gudunar da zaben shugaban kasa, kamar yadda kundin tsarin mulkin kasar ya tanada. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China