Janar Mgwebi, wanda a halin yanzu yake jagorantar rundunar sunturi ta kasar Afrika ta Kudu, zai maye gurbin Laftanal Janar Carlos Alberto dos Santos Cruz dan kasar Brazil ne, wanda ya kammala wa'adin aikin sa a ranar 2 ga watan Disambar shekarar 2015.
A sanarwar ofishin MDD, Janar Mgwebi, yana da kwarewar aiki a cikin gida da kasashen ketare har na tsawon shekaru 35. Ya taba zama kwamandar rundunar MDD a kasar Burundi tsakanin shekarun 2004 zuwa 2006, sannan ya zama jami'i mai kula da sojojin Afrika ta Kudu a shekarun 2007 zuwa 2011.
Mgwebi yana da shaidar karatun Dipolma kan al'amurran tsaro daga jami'ar Afrika ta Kudu.
MONUSCO, ita ce tawagar dakarun wanzar da zaman lafiya a Jamhuriyar demokaradiyyar Congo. Wacce ta maye gurbin MONUC a shekarar 2010. (Ahmad Fagam)