in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An gama kada kuri'a zagaye na biyu a zaben shugaban kasar Nijar
2016-03-21 14:10:05 cri

Da misalin karfe 7 na daren jiya Lahadi ne bisa agogon wurin aka kammala kada kuri'u, a zagaye na biyu na zaben shugaban kasar Nijar. Masu kada kuri'u da suka yi rajista su miliyan 7.5 ne suka kada kuri'unsu, a rumfunan zaben kasar kimanin 25,700, kuma ana sa ran gabatar da sakamakon zaben nan da 'yan kwanaki masu zuwa.

An dai gudanar da zagayen farko na zaben shugaban kasa a Nijar ne a ranar 21 ga watan Fabrairun bana, inda hukumar zabe mai zaman kan ta ta kasar ta sanar a ran 26 ga watan na Fabrairun cewa, shugaba mai ci Mahamadou Issoufou, shi ke kan gaba da kaso kashi 48.41 cikin dari na jimillar kuri'un da aka kada, sai kuma tsohon shugaban majalissar dokokin kasar Hama Amadou wanda ke biye da kashi 17.79 bisa dari na yawan kuri'un da aka kada.

Bisa dokar zaben kasar, wadannan 'yan takara biyu sun shiga fafatawa a zagaye na biyu. Tsakaninsu wanda ya samu mafi yawan kuri'u zai zamo sabon shugaban kasar. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China