Kafin ya sauka babban birnin Nijar, minista Laurent Fabius sai da ya yada zango ranar Asabar a birnin N'Djamena na kasar Chadi da kuma birnin Yaounde na kasar Kamaru, a wani rangadin da ya shafi taka birki ga kungiyar Boko Haram musammun ma a wadannan kasashe uku dake makwabtaka da Najeriya.
Mista Fabius ya samu ganawa tare da shugaban kasar Nijar Mahamadou Issoufou jim kadan bayan saukarsa ranar Lahadi a fadar shugaban kasar dake birnin Niamey.
A yayin taron manema labarai na hadin gwiwa tare da takwaransa na kasar Nijar Bazoum Mohamed, mista Laurent Fabius ya bayyana cewa sakamakon annobar Boko Haram, ya sa kasashen Nijar, Chadi da Kamaru, suka dauki mataki dake nuna himma da kwazo wajen yaki da Boko Haram kuma ya kamata gamayyar kasa da kasa ta nuna yabo kansa.
Ya ce ya zo ne domin kawo taimako da goyon bayan kasar Faransa game da wannan muhimmin mataki da kasar Nijar ta dauka. (Maman Ada)