in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Nijar ta yi alla wadai da harin ofishin jakadancinta dake Cairo
2015-07-30 11:00:16 cri

Gwamnatin kasar Nijar ta yi alla wadai da harin da aka kai wa ginin ofishin jakadancinta dake birnin Cairo na kasar Masar a ranar Laraba, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar dan sanda guda da jikkata mutane uku da suka hada da jami'an tsaro biyu.

A cewar sanarwar ma'aikatar harkokin wajen Nijar, maharan ba wai sun kai harin musammun ba kan Nijar ta hanyar ofishin jakandancinta, amma don farma jami'an tsaron kasar Masar.

Dalili kuwa shi ne, maharan ba su kai ga ginin ofishin jakadancin ba, kana kuma ba su nemi shiga ciki ba, in ji sanarwar.

Kasar Nijar ta yi alla wadai da wadannan hare-haren ta'addanci tare da nuna goyon bayanta ga gwamnatin Masar kan kokarinta da hanyoyin da take dauka domin tabbatar da tsaron jama'a da zaman lafiya a fadin kasar Masar.

A cewar kamfanin dillancin labarai na Masar NEMA, wasu mutane uku dauke da makamai a cikin mota sun bude wuta kan 'yan sanda dake kofar ofishin jakadancin Nijar, a unguwar al-Haram da ke birnin Cairo, tare da kashe a kalla jami'in tsaro guda da raunana biyu, a safiyar Laraba kafin su arta cikin ta kare.

Haka kuma sanarwar ta nuna cewa, harin ya zo daidai da lokacin da kasar ta Masar take fama da hare-haren ta'addanci na wasu kungiyoyin ta'addanci dake nuna biyayya ga kungiyar IS. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China