Da take karbar wannan taimako, ministar harkokin wajen Nijar madam Aichatou Boulama ta tunatar da cewa kasar Aljeriya 'yar uwa ce ga kasar Nijar a ko da yaushe take a shirye domin amsa kiran gwamnatin Nijar domin taimakawa al'ummomin jihar Diffa.
Haka kuma, ministar ta nuna godiya ga gwamnatin Aljeriya bisa wannan tallafi, musamman ma zuwa wakilin minista dake kula da harkokin Afrika da yankin Magreb wanda ya zo da kansa domin isar da wannan taimakon kasarsa zuwa ga kasar Nijar a cikin shirin gaggawa game da jihar Diffa.
A nasa bangare a yayin da yake mika wannan taimako, ministan Aljeriya, ya mika yabo na musammun ga gwamnati da al'ummar kasar Nijar kan yadda suka karbi mutanen Nijeriya da ba su mafaka a kasar Nijar.
Mista Abdoul Kader Messahel ya yi kira ga gamayyar kasa da kasa da masu hannu da shuni da su ba da nasu taimako, domin taimakawa kokarin gwamnatin Nijar wajen kai dauki ga al'ummomin dake jihar Diffa. (Maman Ada)