Da yake jawabi yayin ziyarar da ya kai wurin da ake gudanar da aikin ginin, shugaban kasar ta Nijar Mahamadou Issoufou ya nuna gamsuwa da yadda aikin ke gudana, wanda ya zuwa yanzu ya kai kaso 85 cikin dari.
Rahotanni sun bayyana cewa bayan kammalar aikin, asibitin zai samar da gadajen kwanciya sama da 500, zai kuma baiwa marasa lafiya damar samun jiyya a fannoni daban daban, kama daga masu bukatar jiyyar gaggawa, ya zuwa cututtukan da suka shafi zuciya, da kuma dakunan tiyata 12, baya ga dakunan bincike da sauran su. (Saminu Alhassan)