Shugabar kungiyar Red Cross ta kasar Aljeriya (CRA), Saida Benhabiles, dake kula aikin jigilar wadannan mutane cikin yanayi mai kyau da tsaro, ta sake jaddada cewa ba aikin kora ba ne, amma kasarsa ta amsa bukatar hukumomin Nijar.
A karon farko, kimanin 'yan cin ranin Nijar 400 ake sa ran kwashe su daga Alger zuwa wata cibiyar tattara mutane dake Tamanrasset, gundumar dake kan iyaka da kasar Nijar, kafin wannan aikin jigilar mutanen da zai kai har zuwa 22 ga watan Oktoba, ya shafi sauran yankunan kasar dake fama da kwararar 'yan cin ranin Nijar.
Madam Benhabiles, ta tunatar da cewa an kwashe wani adadin 'yan cin ranin Nijar 3724 da farko zuwa kasarsu, wanda ya hada da yara 900.
Ko da yake babu wani cikakken adadi, a 'yan shekarun bayan nan, miliyoyin 'yan cin rani da suka fito daga Nijar dalilin gudun talauci sun shiga Aljeriya ba bisa doka ba.
Kuma 'yan cin ranin sun warwatsu a fadin kasar Aljeriya, wasu suna zama a sansanoni, wasu kuma sun mamaye hanyoyi da dare ko da rana. Wasunsu na aiki cikin duhu a wuraren gine gine, ko kuma a wasu kamfanonin aikin katako, kere kere da sauran, yayin da kuma musammun ma mata da kananan yara suke yin barace barace a kan tituna. (Maman Ada)