A cewar wata sanarwar ta taron ministoci, burin wannan dubara shi ne na samar a kowace shekara ton dubu 20 na hatsi da kuma kara samar da kudin shiga ga manoma.
Shirin 3N babban shiri ne noma da hukumomin Nijar suka bullo domin kare al'ummar Nijar dada matsalar karancin abinci da yunwa da kuma tabbatar masu yanayin zaman rayuwa mai kayu ta yadda za su halarta ayyukan samar da abinci cikin kasa. Haka kuma wata dama ce ta karfafa karfin kasa na samar da abinci gaban matsalolin karancin abinci da sauran bala'u.
A cewar gwamnatin Nijar, hanya mafi kyau ita ce bunkasa noma rani da kuma zamanintar da kiwo, domin magance kwata kwata matsalolin rashin abinci. Wannan zai yiwu, domin Nijar tana kunshe da albarkatun ruwan karkashin kasa da ruwan dake malala da kuma ruwan sama, in ji shugaban shugaba Mahamadou Issoufou a lokacin bikin rantsar da shi a ranar 7 ga watan Afrilun shekarar 2011. (Maman Ada)