Wata sanarwar da kungiyar 'yan kwadagon kasar ta fitar ta ce 'ya'yan kungiyar sun kadu matuka, bisa kisan bayin Allah a yankin Karamga dake gabashin kasar, lamarin da ake dangantawa da mayakan Boko Haram.
Da yake karin haske game da wannan al'amari, ministan ma'aikatar harkokin cikin gidan kasar Hassoumi Massaoudou, ya ce yayin harin da mayakan kungiyar suka kaddamar a karshen makon jiya, sun hallaka sojoji 46, da wasu fararen hula 28, kana wasu mutane 9 sun jikkata, yayin da kuma ake ci gaba da neman wasu 32 da suka bace.
Tuni dai mahukuntan kasar suka shelanta fara zaman makoki na kwanaki 3 tun daga ranar 29 ga watan Afrilun da ya shude, domin nuna alhinin kisan 'yan kasar.
A baya dai ana gudanar da bukukuwan ranar kwadago a kasar ta Nijar, kamar yadda hakan ke gudana a sassan duniya daban daban. (Saminu Hassan)