Sauran mutane ukun da suka mutu, 'yan asalin kauyen Abadam ne, kamfanin dillancin labaran kasar Sin Xinhua, ya tuntubi majiyar domin sanin adadin wadanda suka mutu daga bangaren maharan, sai dai ba'a bayyana adadin ba, amma an ce maharani sun tsere zuwa wasu sassa na Najeriya wacce ke makwabtaka da Nijar.
Wadannan hare haren na sari ka noke daga Boko Haram a yanki Diffa, suna zuwa ne bayan da hukumomin jamhuriyar Nijar suka ayyana kafa dokar ta baci a yankin Diffa watanni da dama da suka gabata.
Tun a watan Fabrairun wannan shekara, yankunan Bosso da Diffa, wadanda ke makwabtaka da Najeriya ke fama da hare haren Boko Haram babu kakkautawa, lamarin da yayi sanadiyyar rayukan daruruwan fararen hula da kuma jami'an sojoji. Haka zalika, a daidai wannan lokacin, sama da mayakan Boko Haram 1,000 ne sojojin Najar suka hallaka.(Ahmad Fagam)