Gwamnatin Nijar ta shigar a ranar Talata a yayin wani taron ministoci da dokar dake bada damar rattaba hannu kan yarjejeniyar da ta shafi kafa wani kwamitin hadin gwiwa dake hurumin aiwatar da wannan layin iyaka, da aka sanya ma hannu a ranar 5 ga watan Yulin shekarar 2013 a birnin Niamey.
Kwamitin an dora masa nauyin tattara bayyanai da yin nazari kan takardun da ake tsammanin zasu kawo karin haske game da shata layin iyaka tsakanin kasashen biyu, da kuma tattara bayanai da binciken matsalolin dake da nasaba da shari'a, siyasa, tattalin arziki da jama'a, da aiwatar da wannan layin raba iyaka zasu janyo da gabatar da mafita ta yadda za'a daidaita batun, da kuma fara aikin sanya layin raba iyaka.
Bangarorin biyu sun dauki niyyar baiwa kwamitin hadin gwiwa duk wasu takardun da zasu kawo karin haske kan layin raba iyaka tsakanin kasashen biyu. (Maman Ada)