An tura keyar 'yan sanda da dama gidan yari dalilin sumogal din fasfo na jabu a kasar Nijar
'Yan sanda kusan goma na hukumar 'yan sandan kasar Nijar ne, aka gurfanar da su a ranar Jumma'a tare da yanke musu hukuncin zaman gidan yari na shekara daya zuwa shekaru biyar. Hukuncin da babbar kotun birnin Yamai ta fitar, ya gurfanar da mutane biyu, daga cikinsu akwai tsohon darekta janar na larwan fadin kasar, kwamishina Ouba Ibrahim da aka yanke masa zaman gidan yari na shekaru biyar. Sauran mutanen kuma aka yanke musu zaman gidan yari na shekara daya daya. Cikin wannan badakala, dake shafar wadannan ma'aikatan hukumar 'yan sandar Nijar, da ake tsare da su gidan yarin birnin Yamai da kewayensa yau da kusan watanni da dama, kimanin fasfon kasar Nijar dubu daya da dari bakwai ne aka baiwa mutanen kasashen waje daban daban. (Maman Ada)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku