Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya bayyana a jiya Alhamis 17 ga wata cewa, yawan kudin da kasar sa ta kashe wajen aiwatar da matakan soja a kasar Syria cikin tsawon watanni biyar da suka wuce, ya kai dalar Amurka kimanin miliyan 480.
A ganinsa, yanzu haka yawan sojojin da Rasha ta girke a Syria ya wuce bukatar da ake da ita wajen aiwatar da matakan soja. Kaza lika ya ce janye sojojinta daga Syria ya dace da yarjejeniyar da kasarsa ta kulla da gwamnatin Syria. Shugaba Putin ya kara da cewa Rasha, za ta ci gaba da girke sojojinta a wasu sansanoni biyu kadai, don dakile hare-haren da za a iya kaiwa sojojinta.
Dadin dadawa, Mista Putin ya jaddada cewa, Rasha za ta ci gaba da goyon bayan yakin da ake yi da kungiyar IS, da ta Al-Nusra Front, kungiyoyin da kwamitin sulhu na MDD ya ba da tabbacin cewa na 'yan ta'adda ne, inda za ta baiwa gwamnatin Syria taimako irin na kudi, da fasahohi da kuma makamai. (Amina)