in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Putin: Tabbatar da tsagaita bude wuta shi ne abu mafi muhimmanci na kiyaye zaman lafiya a kasar Syria
2016-03-08 10:31:38 cri
Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya bayyana cewa, tabbatar da tsagaita bude wuta shi ne abu mafi muhimmanci na kiyaye zaman lafiya da kyautata yanayin jin kai a kasar Syria.

Bisa labarin da fadar Kremlin ta bayar, an ce, shugaba Putin ya buga waya tare da shugaban kasar Masar Abdel-Fattah al-Sisi a ranar Litinin din nan, inda ya yi bayani game da ayyukan aiwatar da yarjejeniyar tsagaita bude wuta a tsakanin bangarori daban daban na kasar Syria da kasar Rasha ta yi. Kana shugabannin kasashen biyu sun tsaida kudurin ci gaba da yin hadin gwiwa bisa tsarin rukunin aiki na kasa da kasa mai kula da batun Syria, kuma sun jaddada cewa, tilas ne a kara yaki da 'yan ta'addanci dake kasar Syria da Libya da sauran kasashen duniya.

Bisa labarin da kamfanin dillancin labaru na kasar daular Larabawa ya bayar a ranar Litinin, an ce, mai jiran gadon sarauta kuma mataimakin kwamandan sojojin kasar Sheikh Mohamed Bin Zayed Al Nahyan ya gana da ministan harkokin wajen kasar Jamus Frank-Walter Steinmeier a wannan rana a birnin Abu Dhabi, inda suka yi musayar ra'ayoyi kan rikicin kasar Syria, halin kasar Yemen da dai sauransu, kana sun jaddada cewa, kasashen biyu za su kara yin hadin gwiwa wajen yaki da ta'addanci da masu tsattsauran ra'ayi.

A wannan rana kuma, ministan harkokin wajen kasar daular Larabawa Sheikh Abdullah Bin Zayed Al Nahyan ya yi shawarwari tare da takwaran aikinsa na kasar Jamus Steinmeier.

Bayan shawarwarin, minista Abdullah Bin Zayed Al Nahyan ya bayyana a gun taron manema labaru cewa, kasarsa ta nuna goyon baya da a zartas da shirin warware batun Syria ta hanyar siyasa don kawo karshen rikicin kasar.

Kana Steinmeier ya bayyana a gun taron manema labaru cewa, yarjejeniyar tsagaita bude wuta a tsakanin bangarori daban daban na kasar Syria tana da babbar ma'ana, wadda za ta taimakawa wajen sake yin shawarwarin shimfida zaman lafiya a tsakaninsu. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China