in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Rasha ta yi kira ga Amurka da ta dauki nauyin dake wuyanta kan yin watsi da makamai a Syria
2016-03-04 18:31:26 cri
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Rasha Maria Zakharova ta nuna cewa, kasar na fatan Amurka a baki ne kawai ta ce za ta aiwatar da shirinta na B kan batun Syria in dai yarjejeniyar tsagaita bude wuta ta lalace, kuma tana fatan Amurka ta dauki nauyin dake wuyanta yadda ya kamata.

A ranar laraban nan wajen taron manema labaru da aka yi, Maria Zakharova ta ce, kwanan baya wasu manyan jami'an Amurka sun yi kirari cewa, idan an keta yarjejeniyar tsagaita bude wuta a Syria, bangarori masu ruwa da tsaki su koma yin gaban da juna, lalle Amurka za ta dauki shirin ta na B ko kuma wani shiri na daban.

Tace Rasha kuma a nata bangare, tana fatan Amurka ta yi wannan furuci a baki ne kawai, kuma ta kalubanci Amurka da ta dauki nauyin dake wuyanta don gudanar da yarjejeniya yadda ya kamata.

Madam Zakharova ta kuma bayyana cewa, wasu kafofin yada labaru na kasashen yamma na ganin cewa, yarjejeniyar da ake aiwatar yanzu na da wa'adin makonni biyu ne kawai, daga baya bangarori masu ruwa da tsaki za su sake yi gaba da juna. A ganin Rasha, ya kamata a aiwatar da ita ba tare da kayyade lokaci ba.

Ta kara da cewa, ba wanda zai yi iyakacin kokarin neman a sami zaman lafiya cikin makoni biyu kawai. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China