Gwamnatin Syria na dukufa don ganin ta sulhunta da bangaren 'yan adawa. A sa'i daya kuma, bangarori masu ruwa da tsaki suna kokarin dakile 'yan ta'adda a kasar.
Hukumar da ke sa ido kan kare hakkin Bil Adama ta kasar Syria mai hedkwata a birnin London ta bayyana a jiya Asabar 5 ga wata cewa, tashe-tashen hankula sun ragu sosai a cikin wannan mako. Duk da cewa, mutane 135 sun mutu a wuraren da yarjejeniyar ke shafa, amma a sauran wurare wannan adadi ya kai 552, matakin da ya nuna cewa, an samu kyautatuwar zaman lafiya a wannan yanki.
Yayin da ake kokarin tsagaita bude wuta a Syria, gwamnatin kasar kuma na kokarin ingiza manufar samun sulhuntawa tsakanin al'umma. Shugaban kasar Bashar al Assad ya zanta da manema labaru a kwanakin nan baya, inda ya yi kira ga 'yan adawa da su yi watsi da makamai su shiga shawarwari da gwamnati. A nata bangaren kuma gwamnati za ta yafe duk abubuwan da suka faru. (Amina)