in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sojojin gwamnatin kasar Syria sun samu nasara a yakin da suke yi kungiyoyin ta'addanci a wurare daban daban na kasar
2016-03-07 10:44:16 cri
Rundunar sojan kasar Syria ta bayyana cewa, dakarunta sun samu nasara a ci gaba da matakan soja da suke dauka kan kungiyar IS da kungiyar Jabhat al-Nusra, reshen kungiyar al Qaeda dake kasar Syria a wurare daban daban dake arewaci da tsakiya da kuma gabashin kasar.

Kamfanin dillancin labaru na kasar Syria ya ruwaito rundunar sojan tana cewa, sojojin gwamnatin kasar sun yi nasarar lalata sansanin kungiyar Jabhat al-Nusra a wani gari dake da nisan kilomita 50 a kudu maso gabashin birnin Idlib dake jihar Idlib a arewacin kasar Syria, baya membobin kungiyar 11 da suka kashe.

Rundunar sojan ta kuma bayyana cewa, sojojin gwamnatin kasar sun yi nasarar harbe membobin kungiyar Jabhat al-Nusra 7 har lahira tare da raunatar wasu da dama a hare-haren baya-bayan da ta kai a wani kauye da ke kudancin jihar Idlib.

Hakazalika kuma, bangaren soja na kasar Syria ya ce, sojojin gwamnatin kasar sun kai hari ta sama kan sansanoni biyu na kungiyar IS dake tsakiyar jihar Homs, inda suka lalata sansanonin gami da motoci da kuma makamansu. Bugu da kari, sojojin sun kaddamar da wani hari ta sama kan sansanin kungiyar IS dake jihar Deir ez-Zor, inda suka harbe 'yan ta'adda da dama har lahira. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China