Kwamitin sulhun MDD ya zartas da kuduri mai lamba 2268, inda aka amince da yarjejeniyar hana zaman doya da man ja a kasar Syria. Bayan da aka zartas da kudurin, Liu Jieyi ya yi jawabi cewa, zartas da kudurin ya bayyana cewa kasa da kasa suna nuna goyon baya ga warware batun Syria ta hanyar siyasa. Kuma Sin ta yi maraba ga hakan.
Liu Jieyi ya kara da cewa, hanya daya kawai wajen warware rikicin kasar Syria ita ce a warware shi a siyasance. Ya kamata a bi hanyar da ake fuskantar kowane irin yanayi.
Hakazalika kuma, Liu Jieyi ya yi nuni da cewa, kamata ya yi bangarori daban daban na kasar Syria su bi yarjejeniyar hana zaman doya da man ja a kasar Syria, da dakatar da ayyukan tada zaune-tsaye, da gaggauta gudanar da aikin shigar da gudummawar jin kai a yankunan kasar masu fama da rikicin, don samar da sharadi wajen mayar da yin shawarwarin shimfida zaman lafiyar kasar a birnin Geneva cikin hanzari. (Zainab)