in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Syria ya yi kira ga 'yan adawa da su ajiye makamai
2016-03-02 11:22:05 cri

Shugaban kasar Syria Bashar Al-Asaad, ya shaida wa manema labaru a jiya Talata cewa, gwamnatin sa na hakuri ga matakin da 'yan adawa suke dauka na watsi da yarjejeniyar dakatar da musayar wuta, da zummar tabbatar da ci gaba da aiwatar da yarjejeniyar.

Bashar ya ce, rana ta farko da aka aiwatar da yarjejeniyar, wasu 'yan adawa sun karyata ta, amma gwamnatin sa ba ta mayar da martani ba tukuna. Ban da wannan, shugaban Bashar ya yi kira ga dukkanin 'yan adawa da su ajiye makamai su shiga sulhu da gwamnatin.

Kungiyar sa ido kan hakkin Bil Adam a Syria mai hedkwata a birnin London ta ba da labarin cewa, gwamnatin Syria ta fidda takardun kalubalantar 'yan adawa da su yi watsi da makamai da jiragen yaki, su kuma shiga shirin shimfida zaman lafiya.

An ba da labari cewa, wata tawagar 'yan jarida na kasashen waje sun gamu da wani hari da aka kai a ran 1 ga wata a garin Kinsaba na lardin Der ez-Zor, dake arewa maso yammacin kasar Syria mai iyaka da kasar Turkiya, inda 'yan jarida da dama suka ji rauni. A watan Fabrairun da ya gabata, garin dai ya koma karkashin gwamnatin Syria ne bisa taimakon dakarun kasar Rasha. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China