in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Za a jinkirta shawarwarin neman sulhu na Syria zuwa ranar 14 ga watan Maris
2016-03-09 10:22:33 cri
A jiya Talata ne ofishin manzon musamman na MDD dake kula da harkokin Syria ya sanar a birnin Geneva na kasar Switzerland cewa, za a jinkirta shawarwarin neman sulhu na kasar Syria wanda aka shirya gudanarwa a yau Laraba zuwa ranar 14 ga watan nan da muke ciki. Wannan shi ne karo na biyu da aka jinkirta ranar gudanar da shawarwarin neman sulhu na Syria, inda da a karon farko aka dage ganawar daga ranar 7 ga wata zuwa 9 ga wata.

Kakakin ofishin Jessy Chahine ta bayyana a yayin taron maneman labarai da aka yi a birnin Geneva cewa, ba za a sake jinkirta ranar ba. Tun daga yammacin yau ne, manzon musamman kan harkokin Syria Staffan de Mistura da tawagar dake karkashin jagorancinsa za su fara shirya karbar wakilan da za su isa kasar Syria domin halartar taron shawarwarin, inda za su yi shawarwari irin na share fage a tsakaninsu.

Rahotanni na cewa, mai iyuwa ne wakilan da abin ya shafa za su isa kasar Syria bi da bi tun daga ranar 12 ga wata. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China