Bisa labarin da ma'aikatar harkokin wajen kasar Rasha ta bayar a shafin ta na yanar gizo, jami'an masu kula da huldar kasashen waje na kasashen Rasha da Amurka, sun tattauna ne bisa umarnin shugaban kasar Rasha Vladimir Putin, da na Amurka Barack Obama.
A lokacin ne kuma suka nazarci matakan da suka dace a kara dauka domin daidaita ra'ayoyin bangarorin 2 dangane da batun Syria, ta yadda za a samu damar karfafa yarjejeniyar tsagaita bude wuta, da hana abkuwar abubuwan da suka saba wa yarjejeniyar, da samar da karin hanyoyi na samar da tallafin jin kai, gami da taimakawa kokarin warware rikicin Syria ta hanyar siyasa.
Haka zalika an bayyana cewa yayin zantawar Mr. Lavrov da Al-Jubeir na Saudiyya, Al-Jubeir din ya yaba wa matakan da kasar Rasha ta dauka. Sa'an nan ya ce kasarsa na goyon bayan matakan da aka dauka na tabbatar da cewa bangarorin kasar Syria sun yi biyayya ga yerjejeniyar tsagaita bude wuta, gami da ci gaba da kokarin yaki da kungiyoyin 'yan ta'adda. (Bello Wang)