Wakilin musamman na MDD mai kula da batun Syria Mista Staffan de Mistura ya bayyana a ranar Talata cewa, matakin da Rasha ke dauka a wannan karo ya kasance wani ci gaba mai kyau, shi kuma yana fatan matakin zai kawo tasiri mai kyau ga shawarwarin da aka yi a birnin Geneva game da shimfida zaman lafiya a kasar Syria.
Ban da haka kuma, a cewar ma'aikatar harkokin wajen kasar Faransa, tana maraba da ko wane matakin da za a dauka don warware rikicin Syria, kuma tana fatan matakin da Rasha ke dauka zai sassauta halin da Syria ke ciki. Ban da wannan kuma, a nashi bangare, ministan harkokin waje na kasar Iran wanda ke ziyarar aiki a kasar Austriliya Mista Mohammad Javad Zarif ya ce, janye sojojin da Rasha ta yi ya kasance wani sako mai kyau ne ga yunkurin shimfida zaman lafiya a Syria. (Amina)