in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An tsaida 9 ga watan nan a matsayin sabon rana na tattaunawar Syria
2016-03-02 10:13:16 cri
Ofishin Manzon musamman na Magatakardar MDD akan kasar Syria a ranar talatan nan ya sanar da cewar Staffan de Mistura na shirin sake tattaunawar cikin gida na samar da daidaito a kasar Syria a ranar 9 ga wata.

Kamar yadda sanarwar da aka fitar ya bayyana , za'a farfado da tattaunawar zaman lafiyan ne da zummar samar da isashen lokaci da za'a shawo kan al'amurra a kasar, wanda a yanzu Manzon musamman na magatakardar MDD ya tsaida ranar 9 ga wannan watan don yin haka.

Manzon na MDD tun da farko yayi fatan farfado da tattaunawar ne a ranar 7 ga wata bayan da MDD ta jagoranci tattaunawa da za'a samar da maslahar siyasa a kasar tsakanin gwamnatin Shugaba Bashar al- Assad da bangaren dakarun adawa, wanda ya samu tsaiko ba shiri a ranar 3 ga watan fabrairu bayan da dukkan bangarorin suka gagara ganin juna gaba da gaba akan wassu batutuwa.(Fatimah Jibril)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China