Manzon musamman akan kasar Syria na MDD Staffan de Mistura a daren ranar jumm'an nan bayan yi ma kwamitin tsaron majalissar bayani game da halin da ake ciki na tattaunawar cikin gida na kasar Syria ya bayyana cewa an tsaida ranar 7 ga watan Maris a matsayin ranar da za a farfado da shawarwari idan an iya aiwatar da yarjejeniyar tsagaita bude wuta yadda ya kamata.
Mr. Mistura a lokacin ganawa da manema labarai ya kuma bayyana cewa za'a yi taro akan tsagaita bude wuta a yau Asabar domin sa ido akan yadda za'a aiwatar da dakatar da zaman doya da manjan, bisa ga yarjejeniyar da kungiyoyi 97 masu dauke da makamai da kuma gwamnatin Syrian suka amince da shi, wadda kuma ta samu goyon bayan yankuna da hukumomin kasashen duniya.