Bokova, wadda ta bayyana hakan yayin taron yini biyu, na dandalin Ilimi da bunkasa samar da sana'o'i na bana, wanda da ya gudana a jiya Asabar, ta kara da cewa munanan hotuna da faya-fayan bidiyo dake nuna yadda mayakan IS ke rushe wuraren adana kayan tarihi a Syria da Iraqi, na da matukar tada hankali, kuma dukkanin sassan duniya na da rawar takawa game da warware rikicin kasashen biyu
A cewar ta wani sakamakon bincike da UNESCO ta gudanar, ya nuna cewa akwai a kalla yara kanana maza da mata miliyan 250 a duniya, wadanda ba sa iya karatu da rubutu, duk kuwa da cewa sun kammala shekaru 4 a makarantun firamare. Hakan ne ma ya sa a cewar Bokova, UNESCO ke da wani shiri na nan da shekara ta 2030 game da samar da ilimi, shirin da ke da nufin bunkasa ilimin al'ummar duniya baki daya.
Ta ce ana fatan daukar wannan mataki zai samar da al'ummun duniya da za su iya ilmantar da 'ya'yan su, tare da koyar da su juriya da martaba kayan da aka gada kaka da kakanni.(Saminu Alhassan)