Haka kuma, kwamitin yana ganin cewa tsagaita bude wutar na makonni biyu zai taimakawa kungiyoyinsu wajen bincike game da yadda gwamnatin kasar ke gudanar da yarjejeniyar.
Ma'aikatar harkokin wajen Syria ta sanar a ranar Talatar da ta gabata cewa, gwamnatin kasar ta amince da yarjejeniyar tsagaita bude wuta, amma ba za ta dakatar da matakan soja da ta ke dauka kan kungiyoyin IS da al-Qaeda dake kasar ba.
Bugu da kari ta sanar da cewar, kasar za ta tattauna da Rasha wajen tabbatar da wadanne yankuna da kungiyoyi ne dake kunshi cikin yarjejeniyar, domin aiwatar da yarjejeniyar cikin lokaci kuma yadda ya kamata. (Maryam)