A ran 22 ga wata ne kasashen Amurka da Rasha, suka kulla yarjejeniyar tsagaita bude wuta a kasar Syria, wadda za a fara gudanarwa a ranar 27 ga wata.
Kaza lika, bisa sanarwar da kasashen biyu suka bayar cikin hadin gwiwa, an ce kamata ya yi bangarorin da rikicin kasar Syria ya shafa, su nuna amincewarsu da yarjejeniyar kafin karfe 12 na daren ranar 26 ga wata. Sai dai a gefe guda za a ci gaba da yaki da reshen kungiyoyin IS da al-Qaeda, da dai sauran kungiyoyin ta'addanci, wadanda kwamitin sulhun MDD ya sa su cikin jerin kungiyoyin 'yan ta'adda a kasar. (Maryam)