in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta zartas da kudurin yanke hukunci kan ma'aikatanta wadanda suka ci zarafin mata
2016-03-12 13:26:48 cri
A jiya Juma'a 11 ga wata, kwamitin sulhu na MDD ya zartas da wani kudurin kara karfin hukunta ma'aikatanta da suka ci zarafin mata, inda ya zama a karon farko da ya fitar da kudurin kan wannan batu.

Wannan daftarin da Amurka ta gabatar ya sami amincewa daga mambobin majalisar 14, saura daya wato Masar wadda ta yi watsi da kuri'ar ta kan wannan batu.

Wannan kuduri kuma ya ba da izni ga MDD da ta dakatar da aikin wata rundunar kiyaye zaman lafiya idan sojojinta sun ci zarafin wasu. A sa'i daya kuma, babban magatakardan MDD Mista Ban Ki-Moon na da ikon cire gaba dayan sojojin da aka tura, idan suka aiwatar da laifin kuma kasashen da suka tura wadannan sojoji basu dauki ko wani mataki kan batu ba.

Saboda MDD ba ta da tsarin aiwatar da dokokin shari'a ba, hakan ya sa idan masu aikin kiyaye zaman lafiya sun aikata laifi kuma an kai shi gaban kotu, kasashen da suka tura wadannan sojoji kawai ke da ikon yanke masu hukunci.

Wakilin dindindin na kasar Sin dake MDD, Mista Liu Jieyi ya bayyana bayan da aka kada kuri'un cewa, Sin na goyon bayan manufar da Ban Ki-Moon ya dauka babu sassauci kadan ga wadanda suka aikata wannan laifi, tare kuma da daurewa kasashen duniya gindi da su dauki matakan da suka dace. Sa'an nan, tana goyon bayan rawar da kwamitin sulhu ke taka da kuma ya kara hadin gwiwa da taron MDD da dai sauran hukumomi.

An ba da labari cewa, a bara akwai ayyukan cin zarafin mata 99 da ma'aikatan majalisar ke da hannu a ciki, kuma 69 daga cikinsu na shafar masu aikin kiyaye zaman lafiya, wanda ya karu da sau 19 bisa na shekarar 2014. Daga cikinsu kuma, ayyukan da shafar ma'aikatan rundunar kiyaye zaman lafiya dake Kongo Kinshasa ya fi yawa, inda suka kai 7. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China