in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ban Ki-moon ya nada jami'ar da za ta binciki zargin cin zarafin yara a CAR
2016-02-09 11:43:04 cri
Babban magatakardan MDD Ban Ki-moon ya nada Jane Holl Lute 'yar kasar Amurka a matsayin jami'a ta musamman da za ta binciki batun cin zarafin yara kanana da ake zargin dakarun MDD da ke aikin warzar da zaman lafiya a Jamhuriyar Afirka ta tsakiya da aikatawa.

Kakakin MDD Stephane Dujarric wanda ya bayyana hakan ga taron manema labarai, ya ce nada Madam Lute wani bangare ne na matakan da babban magatakardan na MDD yake dauka domin bitar rahoton da kwamiti mai zaman kansa ya gabatar a ranar 17 ga watan Disamban shekarar 2015 game da wannan batu.

Kakakin na MDD ya bayyana cewa, Mr Ban ya himmantu wajen ganin an magance dukkan matsaloli da aka gano a kan lokaci, kana a dawo da martabar dakarun dake gudanar da ayyukan kiyaye zaman lafiya a duniya.

Ana fatan a lokacin da take gudanar da ayyukanta a wannan shekara, Madam Lute za ta taimakawa kokarin da babban magatakardan MDD da sauran ofisoshi, shirye-shirye, asusu da sassan MDD suke yi na inganta ayyukan dakarun wanzar da zaman lafiya na MDD da tsare-tsaren kare hakkin bil-adam, ta yadda za a karfafa matakan da MDD take dauka game da batun cin zarafin mata da yara. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China