A cikin wani rahoton da za a fitar ba da jimawa ba, masu bincike na MINUSCA sun tattara bayanai masu muni sosai kan ayyukan cin zarafin dan Adam da aka gudanar daga ranar 26 ga watan Satumba zuwa 20 ga watan Oktoban shekarar 2015 a Afrika ta Tsakiya, in ji wata sanarwar MINUSCA.
Haka kuma, sun gano lalata da karbe kaddarori, har ma da cinna wuta a gidaje da dama tare da sace kayayyakin wasu kungiyoyin gwamnati da na kungiyoyi masu zaman kansu, a cewar wannan sanarwa.
Shugaban tawagar MINUSCA, Parfait Onanga-Anyanga, ya bayyana damuwarsa game da iyuwar ko masu hannu kan wadannan ayyukan keta hakkin dan Adam ko za su amfana da rashin hukunta su, da kuma yin kira ga hukumomin Afrika ta Tsakiya da su dauki matakan gaggawa yadda ya kamata domin gurfanar da masu hannu kan wadannan munanan ayyuka gaba kotu. (Maman Ada)