in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wakilin Sin ya bayyana ra'ayin Sin game da batun inganta tsarin kare hakkin dan Adam
2016-03-11 11:01:50 cri
A jiya ne mukaddanshin jakada na tawagar wakilan Sin dake birnin Geneva Fu Cong ya yi jawabi a yayin taro na 31 na majalisar kare hakkin dan Adam ta MDD game da rahoton aiki na shekara-shekara na ofishin kula da harkokin hakkin dan Adam na MDD, inda ya bayyana ra'ayin Sin kan yadda za a inganta matakan kare hakkin dan Adam ta yadda za a kiyaye muhimmin matsayi na aikin kare hakkin dan Adam, da kuma kyautata ayyukan ofishin kula da harkokin hakkin dan Adam na MDD.

Game da yadda za a inganta tsarin kare hakkin dan Adam, Fu Cong ya bayyana cewa, a ganin kasar Sin, abu mafi muhimmanci shi ne tabbatar da 'yancin tsarin kare hakkin dan Adam na duniya, da daina yin amfani da ma'auni biyu kan wannan batu.

Ya ce, muddin ana bukatar a kiyaye muhimmin matsayi na aikin kare hakkin dan Adam, ya kamata a tabbatar da yin hadin gwiwa, da daina kwace albarkatu daga sauran fannoni, da girmama muhimmin matsayi na hukumomin MDD da abin ya shafa, da kuma barin gwamnatocin kasa da kasa su kasance a kan gaba wajen kiyaye muhimmin matsayi na wannan aiki.

Hakazalika kuma, Fu Cong ya bada shawara kan yadda za a kyautata ayyukan ofishin kula da harkokin kare hakkin dan Adam na MDD. Ya ce, kamata ya yi ofishin ya gudanar da ayyukansa bisa iznin da babban taron MDD ya bayar, da dora muhimmanci ga yin mu'amala tare da kasashe membobin MDD, da magance bayar da bayanai marasa tushe. Don haka kamata ya yi ofishin ya gudanar da bincike kan dukkan fannonin da abin ya shafa. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China