in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ban Ki-moon yana fatan dukkan kasashen duniya su sauke nauyin tinkarar kalubalen jin kai tare
2016-02-10 12:57:24 cri
A jiya Talata ne, Mr. Ban Ki-moon, magatakardan MDD ya fitar da wata sanarwa gabanin taron kolin kasashen duniya kan batun jin kai da za a yi a watan Mayu mai zuwa, inda ya yi kira ga kasashen duniya da su dauki nauyi tare wajen tinkarar kalubalen jin kai da ake fuskanta a duk fadin duniya.

A wannan rana, an shirya wani taron a MDD, inda aka saurari wani rahoto mai taken "kowa yana da hakki wajen taimakawa harkokin jin kai a duniya" da Ban Ki-moon ya gabatar. A cikin rahotonsa, Ban Ki-moon ya bayyana cewa, yanzu kasashen duniya na fuskantar kalubaloli masu sarkakiya kuma masu tsanani, kamar tsattsaurar rayoyin nuna karfin tuwo, da ta'addanci da munanan laifukan da ake aikata tsakanin kasa da kasa, da bala'u daga indallahi da su kan faru sakamakon sauyin yanayin duniya, da kuma babban gibin dake tsakanin masu arziki da matalauta da yake kara tsananta. Sakamakon haka, yanzu ana bukatar taimakon jin kai, amma har yanzu, ba a bullo da dabarun warware wadannan matsaloli a siyasance ba.

Sannan a cikin rahoton da Ban Ki-moon ya gabatar wa babban taron MDD, yana fatan kasashen duniya su mai da hankali kan ayyukan da za su shafi fannoni 5, wato dole ne shugabannin kasashen duniya su bullo da matakan yin rigakafi da kawo karshen rikice-rikice da ke faruwa, haka kuma dole ne kowace kasa ta sauke nauyin kare rayukan bil Adama. Bugu da kari, dole ne a sa niyyar neman samun ci gaban dukkan al'ummomin duniya. Sannan su yi kokarin canja salon zaman rayuwar al'ummominsu, da kuma taimaka musu wajen kawo karshen neman taimako. Daga karshe, Mr. Ban yana fatan a kara karfin kananan hukumomi na tinkarar kalubaloli.

A karshen watan Mayu mai zuwa ne ake sa ran za a yi taron kolin kasashen duniya kan batun jin kai a birnin Istambul na kasar Turkiya. (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China