An kaddamar da harin ne kan ofishin na MINUSMA wanda ke garin Kidal a arewacin Mali a ranar Jumma'ar da ta gabata.
A sanarwar da mai magana da yawun magatakardan MDD ya fitar, ya bayyana kaddamar da hare hare kan jami'an aikin wanzar da zaman lafiya a matsayin yin keta dokokin kasa da kasa da suka haramta aikata laifukan yaki, sannan ya bukaci gwamnatin Mali da ta gaggauta gudanar da bincike domin zakulo wadanda ke da hannu a kai harin domin hukunta su.
Ban, ya kara da cewa kaddamar da hari kan ofishin na MINUSMA, ba zai taba sanyaya gwiwa MDD ba a yunkurinta na tallafawa gwamnatin kasar Mali domin samun dawwaumamman zaman lafiya da tsaron rayukan al'ummar kasar. (Ahmad Fagam)