in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ya kamata a karfafa wakilci na kasashen Afirka a MDD, in ji wakilin Sin
2016-02-23 11:24:44 cri
Zaunannen wakilin kasar Sin dake MDD Liu Jieyi ya bayyana a ranar Litinin din nan cewa, ya kamata kwamitin sulhu na MDD ya mai da hankali kan karfafa wakilci na kasashe masu tasowa, musaman ma kasashen Afirka a yayin da yake yin kwaskwarima, kuma ya kamata a kara shigar da kanana da matsakaitan kasashe cikin kwamitin.

A wannan rana, babban taron MDD ya yi taro zagaye na biyu game da shawarwari a tsakanin gwamnatocin kasa da kasa kan aikin kwaskwarimar kwamitin sulhu na MDD, inda Liu Jieyi ya bayyana cewa, bisa kundin tsarin mulkin MDD, an ce, mambobin kasashen MDD sun baiwa kwamitin sulhu na MDD babban alhakin kiyaye zaman lafiya da tsaron kasa da kasa, kwamitin sulhu na MDD ne ya dauki alhakin yadda ya kamata a madadin mambobinsa. Cikin shekaru 70 da aka kafa MDD, an sami babbar canjawa kan mambobinta, adadin mambobin MDD ya karu daga 51 zuwa 193, kuma galibin daga cikinsu su ne kasashe masu tasowa, haka kuma, galibin harkokin da aka yi bincike cikin kwamitin sulhu na MDD sun shafi kasashe masu tasowa, musamman ma kasashen Afirka.

Sabo da haka, ya kamata a habaka wakilci na kasashe masu tasowa, musamman ma kasashen Afirka cikin kwamitin sulhu na MDD, da kuma bai wa kananna da matsakaicin kasashe damar shiga kwamitin sulhu na MDD, domin ba da shawara musu a yayin da ake yanke kuduri a kwamitin.

Bugu da kari, ya kamata kwamitin sulhu ta nuna adalci a yayin da yake zabin mambobinsa a yankuna daban daban, tun da aka fara shawarwari a tsakanin gwamnatoci a shekarar 2009, mambobin kasashen sun ba da shawarwari da dama game da yadda za a kyautata tsarin kwamitin, muna fatan za a iya ci gaba da zurfafa tattaunawarmu kan wanna batu a nan gaba. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China