Mista Liu Jieyi, ya furta hakan ne a lokacin babban taron MDD, ya bayyana cewar kungiyoyin 'yan ta'adda na yin amfani da shafukan yanar gizo wajen isar da sakonninsu na muryoyi, da yada akidunsu na tsattsaurin ra'ayi, da daukar ma'aikata da tattara kudaden da suke amfani da su da kuma gudanar da ayyukan ta'addaci, don haka Liu ya nuna bukatar daukar matakai domin dakile aniyar kungiyoyin 'yan ta'adda.
Wakilin na kasar Sin na dindindin a MDD, ya bukaci kasashen duniya da hukumomin MDD masu ruwa da tsaki, da su dauki tsauraran matakai game da dokokin da suka shafi amfani da shafukan yanar gizo domin dakile aniyar 'yan ta'adda.
Sannan ya bukaci bangarorin da abin ya shafa, da su yi aiki kafa da kafa wajen yakar ayyukan ta'addanci.
Liu ya ce, sam bai kamata mu danganta wata kabila ko addini da ayyukan ta'addanci ba. (Ahmad Fagam)