Mr. Liu ya bayyana hakan ne a jiya Alhamis, yayin zaman kwamitin tsaron MDD, yana mai cewa hanyoyin diflomasiyya su ne mafiya dacewa maimakon barazana ko sanya takunkumi.
Kaza lika manzon na Sin ya bayyana cewa, ya dace a rika sauraron ra'ayoyin sassan da ke fuskantar tashe tashen hankula, wanda hakan ne kadai zai baiwa kwamitin tsaron damar daukar matakai mafiya dacewa. Har wa yau ya yi kira ga kwamitin tsaron da ya maida hankali ga magance manyan dalilan dake haifar da barazana ga tsaro da zaman lafiyar duniya, kamar yadda hakan ke kunshe cikin dokokin MDD.
Daga nan sai ya jaddada bukatar tuntubar mambobin kwamitin tsaron kan dukkanin manufofi, da matakan da ake nazarta, domin samun cikakken hadin kai a ayyukan kwamitin. (Saminu Alhassan)