Kwamitin sulhun MDD ya gudanar da taro a wannan rana, inda aka saurari sanarwar da shugaban kungiyar kiyaye tsaro da hadin gwiwa ta Turai wato OSCE, kuma ministan harkokin wajen kasar Jamus Frank-Walter Steinmeier ya gabatar.
A cikin jawabin sa, Liu Jieyi ya bayyana cewa, Sin na fatan za a kai ga warware batutuwan yankuna ta hanyar gudanar da shawarwari, ko ma sauran hanyoyi na siyasa, tare da nuna goyon baya ga kungiyoyin yankuna wajen aiwatar da manufofin harkokin waje na kiyaye tsaro, da warware matsaloli cikin lumana, don samar da gudummawa wajen sa kaimi ga kiyaye zaman lafiya a yankuna daban daban.
Liu Jieyi ya bayyana cewa, yanzu haka ana daukar matakan kiyaye zaman lafiya a yankin gabashin kasar Ukraine, kasancewar bangarori daban daban ciki har da kungiyar OSCE sun yi namijin kokari a wannan fanni.
Ya ce domin cimma burin warware takaddamar Ukraine ta hanyar siyasa, ya kamata a yi la'akari da bukatun yankuna da kabilu daban daban na kasar ta Ukraine, a kuma dora muhimmanci kan kulawar bangarori daban daban da abin ya shafa ke nunawa. A cewar sa Sin na goyon bayan bangarori daban daban, game da aniyar su ta aiwatar da kuduri mai lamba 2202, wanda kwamitin sulhun MDD ya zartas, da aiwatar da yarjejeniyar Minsk, da kuma ingiza yunkurin warware batun ta hanyar siyasa. Don haka ya dace kasashen duniya su nuna goyon bayan su ga tsarin shiga-tsakani na Normandie, wanda ya taka muhimmiyar rawa kan batun, da sa kaimi wajen gaggauta cimma burin samun zaman lafiya, da bunkasuwa a kasar Ukraine. (Zainab)