in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jakadan Sin ya jaddada muhimmancin mutunta yarjejeniyar MDD
2016-02-16 11:34:16 cri
Wakilin dindindin na kasar Sin a MDD, mista Liu Jieyi,ya bukaci kasashen duniya su kare matsayin su game da yarjejniyar MDD bisa la'akari da muhimmancin yarjejeniyar, duba da irin yanayin da duniya ke ciki a halin yanzu.

Liu Jieyi, ya fada a taron kwamitin sulhu MDD cewar, wannnan yarjejeniya an bijiro da ita ne bayan barnar da yakin duniya na biyu ya haddasa. Kuma yarjejeniyar ta kunshi wani jadawali ne wadda al'ummar kasashen duniya suka yi na'am da shi, domin yin aiki tare da nufin sake gina duniyar bil adama da kawata ta.

Ya kara da cewar, yarjejeniyar MDD a wannan zamani ta kasance a matsayin wani abu dake da matukar tasiri, kuma wanda ya dace da yanayin da ake ciki a duniya a halin yanzu.

Kwamitin mai mabobi 15, ya gudanar da taron muhawara na ministoci ne mai taken mutunta yarjejeniyar MDD a matsayin sahihiyar hanyar da zata wanzar da zaman lafiya da tsaro a duniya.

Wakilin na kasar Sin ya fada cewa, muddin ana bukatar mutunta manufofin dake kunshe cikin yarjejeniyar, ya zama tilas kasashen duniya su yi aiki kafada da kafada ta hanyar kiyaye dokoki da mutunta juna a yayin mu'amala tsakanin kasa da kasa.

Liu ya kara da cewar, wasu daga cikin muhimman kudororin dake kunshe cikin yarjejeniyar sun hada da, mutunta 'yancin gashin kai na kasashe, da gujewa yin katsalandan ga sha'anin gudanarwar kasashe, da kuma warware duk wata takaddama dake wanzuwa tsakanin kasashen duniya, wadannan na daga cikin muhimman al'amurran da suka shafi kiyaye dokokin kasa da kasa, inji mista Liu.

Ya kara da cewar akwai bukatar a dauki matakan tabbatar da hadin kai tsakaninn kasashen duniya ta kowace fuska, sannan a yi watsi da duk wani batun da zai haddasa yakin cacar baka.

Mista Liu ya ce, abin da yafi muhimmanci a mayar da hankali kan sa shi ne, rungumar sabon salo na hadin gwiwa tsakanin kasa da kasa da kuma shiyya da shiyya domin cin moriyar juna da samun bunkasuwa ga al'ummar duniya.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China