Sakatare Janar na MDD Ban Ki-moon ya bukaci kasashen duniya sun sanya hannu kan yarjejeniyar sauyin yanayi ta Paris wanda ake sa ran gudanar da bikin rattaba hannu kan yarjejeniyar a ranar 22 ga watan Afrilun wannan shekara a birnin New York.
Ban ya yi wannan kiran ne gabanin bikin sanya hannun da ake sa ran gudanarwa, tun bayan amincewa da daftarin yarjejeniyar ta COP21 a lokacin babban taron kasashen duniya kan sha'anin sauyin yanayi a watan Disambar shekarar bara a birnin Paris, taron wanda ya kasance mai cike da dunbun tarihi da aka gudanar kan sauyin yanayi.
Ya kara da cewar, matakin zai taimaka wajen kara kaimi domin rage dumamar yanayi a duniya zuwa kasa da maki 2 a ma'aunin Selshiyas.
Ban ya shawarci kasashen duniya da su baiwa bikin na ranar 22 muhimmci, kasancewa shi ne mataki na gaba game da tinkarar matsalar sauyin yanayi. Sannan ya kara da cewar, ana sa ran a shekarar nan ta 2016, za'a aiwatar da jawaban da aka gudanar da ke kunshe cikin yarjejeniyar taron na birni Paris a aikace.
Ban ya ce ana sa ran shugabannin kasashen duniya za su maida hankali kan batutuwa hudu kamar haka: aiwatar da yarjejejniya kan sauyin yanayi, da rage dumamar duniya zuwa kasa da kashi biyu a ma'aunin Selshiyas, da tsara jadawalin bibiyar yarjejeniyar ta Paris, sai kuma tsawaita wa'adin shirin yaki da sauyi yanayi zuwa shekarar 2020.(Ahmad Fagam)