A sanarwar da kwamitin ya fitar, ya bukaci gwamnatin Mali da ta gaggauta gudanar da bincike domin zakulo wadanda ke da hannu a kai harin domin hukunta su.
Kwamitin mai mutane 15 ya bayyana kaddamar da hare hare kan jami'an aikin wanzar da zaman lafiya a matsayin yin karan tsaye ga dokokin haramta laifukan yaki na kasa da kasa.
Sanarwar ta bayyana dukkan nau'in hare haren ta'addanci a matsayin manyan abubuwan dake yin baraza ga zaman lafiyar duniya.
A yanzu a kara tsaurara tsaro a yankin tun bayan kaddamar da wadannan hare hare. (Ahmad Fagam)