in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Rasha ya Gana da Ministan harkokin wajen Sin
2016-03-12 13:16:22 cri
A jiya Juma'a 11 ga wata, shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya gana da ministan harkokin waje na kasar Sin Mista Wang Yi wanda ke ziyarar aiki a kasar.

Yayin ganawar tasu, Mr. Putin ya darajanta dangantakar dake tsakanin kasashen biyu, ya ce, Rasha na fatan kara tuntubar kasar Sin cikin harkokin duniya da hadin gwiwa wajen kiyaye ka'idar nauyin kasa da kasa.

A nasa bangare kuwa, Mista Wang ya ce, kasancewar wannan shekara aka cika shekaru 15 da kulla yarjejeniyar dangantakar sada zumunci tsakanin Sin da Rasha, Sin na fatan yin amfani da wannan zarafi mai kyau domin kara zurfafa dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu bisa manyan tsare-tsare a dukkanin fannoni.

Ban da wannan kuma, Mista Wang ya kuma gana da takwaransa na kasar Rasha Sergei Lavrov a wannan rana. Yayin da suka zanta da manema labaru bayan ganawa tasu, Mista Wang Yi ya bayyana kwarin gwiwar sa sosai don ganin makoma mai kyau ga bunkasuwar dangantakar dake tsakanin kasashen biyu nan gaba. Ban da wannan kuma, Mista Wang da Sergei Lavrov sun yi musanyar ra'ayi kan halin da zirin Koriya ke ciki, kuma sun kai ga matsaya daya kan kawar da makaman nukiliya a zirin, kuma suna kokarin taka rawarsu wajen farfado da shawarwari tsakanin bangarori shida masu ruwa da tsaki game da wannan batu. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China