Shugaban kasar Guinea Alpha Conde ya gana da ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi jiya Litinin a fadarsa da ke birnin Conakry.
A yayin ganawar, Wang Yi ya furta cewa, kasar Sin ta ba da taimako cikin lokaci yayin da cutar Ebola ta barke a kasar Guinea, haka zakila, Sin za ta jagoranci tallafa wa Guinea wajen samun ci gaban tattalin arziki da ma zamantakewar al'umma bayan barkewar cutar, musamman ma a fannonin warware matsalolin ci gaban muhimman ababen more rayuwa da karancin kwararru. Kana Sin za ta hada kai tare da Guinea wajen raya masana'antu da ingancin abinci da kiwon lafiyar jama'a, a kokarin inganta zaman rayuwar jama'ar kasar Guinea a fannonin aikin yi, abinci, gami da kiwon lafiya.
A nasa jawabin, shugaba Gonde ya godewa kasar Sin bisa ga babban taimakon da ta baiwa kasar a lokacin da cutar Ebola ta barke a kasar. Kana ya ce, Guinea ta riga ta fara aikin sake farfado da kasar bayan barkewar cutar, inda ta himmatu wajen inganta hadin gwiwa tare da kasar Sin domin kara karfinta na samun bunkasuwa.(Kande Gao)