in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wang Yi: Sin tana son bude hadin gwiwa a fannoni daban daban a tsakanin ta da Liberia
2015-08-10 13:21:33 cri
Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya bayyana a gun taron manema labaru da aka gudanar a birnin Monrovia dake kasar Liberia a jiya Lahadi cewa, Sin tana son bude hadin gwiwa a fannoni daban daban a tsakanin ta da Liberia bayan da Liberia ta yi nasarar kawar da cutar Ebola.

Wang Yi ya bayyana cewa, kasar Liberia tana bukatar goyon baya daga kasashen duniya wajen sake gina tattalin arziki da zamantakewar al'ummar kasar. Kasar Sin tana son bin hanyar samun moriyar juna, da bude hadin gwiwa a tsakaninta da kasar Liberia bisa bukatu da amincewar kasar ta Liberia.

Wang Yi ya kara da cewa, muhimmiyar hanyar hana sake barkewar cututtuka kamar cutar Ebola ita ce bullo da matakan kawar da talauci da samun bunkasuwa cikin hanzari. Kuma a yayin da ake kokarin daukar wadannan matakai, Sin a shirye ta ke ta hada gwiwa da kasashen Afirka. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China