in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ministan harkokin wajen kasar Sin zai kai ziyarar aiki a nahiyar Afrika
2016-01-28 19:16:05 cri
Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Madam Hua Chunying, ta sanar da cewa bisa gayyatar da takwarorinsa na kasashen Malawi, da Mauritius, da Mosambique da Namibiya suka ba shi, ministan harkokin waje na kasar Sin Wang Yi zai kai ziyarar aiki a kasashen hudu daga ranar 30 ga watan nan na Jarairu ya zuwa ranar 6 ga watan Fabrairu. Ban da wannan kuma, Mista Wang zai halarci taron baiwa kasar Syria tallafin jin kai, wanda za a shirya a ranar 4 ga watan Fabrairu a kasar Birtaniya.

Game da tambayar da aka gabatar mata, cewa mene ne dalilin da ya sanya ministan harkokin wajen kasar Sin ya kan kai ziyararsa ta farko a cikin sabuwar shekara a kasashen Afirka a shekarun baya baya nan. Mistan Hua ta ce, bunkasa hadin kai da kasashen Afirka babban tushe ne na manufar diplomasiyyar kasar Sin, kuma hakan ya zama wani tsari da Sin take nacewa cikin dogon lokaci. Ta ce ministan harkokin waje na kasar Sin ya kan kai ziyararsa ta farko cikin wata sabuwar shekara kasashen Afirka, kuma Mr. Wang ya rungumi wannan mataki, domin nuna babban muhimmancin da Sin take dorawa kan raya dangantaka tsakanin ta da Afirka.

Madam Hua ta kara da cewa, muhimmin aiki da mista Wang zai gudanar a wannan karo shi ne, tattauna da shugabanni da ministocin harkokin waje na kasashen hudu, domin tabbatar da yarjeniyoyin da aka daddale a taron kolin dandalin tattaunawar hadin kai tsakanin Sin da Afrika da aka gudanar a Johannesburg, musamman game da sabbin matakan da shugaba Xi ya gabatar a taron kolin, ciki hadda sabbin tunani da ra'ayoyin raya dangantakar dake tsakanin bangarorin biyu, da shirye-shirye goma na hadin gwiwa da za a gudanar a cikin shekaru uku masu zuwa da dai sauransu, ta yadda jama'ar bangarorin biyu za su amfana da hadin gwiwarsu. (Amina)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China