in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ministan harkokin waje na kasar Sin ya yi musayar ra'ayi da takwaransa na kasar Rasha ta wayar tarho
2016-02-06 09:17:55 cri

Ministan harkokin waje na kasar Sin Wang Yi ya yi musayar ra'ayi tare da takwaransa na kasar Rasha Sergei Lavrov ta wayar tarho kan huldar dake tsakanin kasashen biyu da kuma batutuwan da suka fi jawo hankulan su.

Bangarorin biyu sun jinjina sakamakon da aka samu wajen raya huldar abokantaka a tsakanin kasashen su bisa manyan tsare-tsare, suka ce ya kamata shugabannin kasashen Sin da Rasha su ci gaba da kai ziyarar juna da kara yin musayar ra'ayi da zurfafa hadin gwiwa da kuma kiyaye moriyarsu.

A game da batun nukiliya na zirin Koriya, bangarorin biyu suna ganin cewa, ya kamata bangarori daban daban su sake yin shawarwari kan batun nukiliya na zirin Koriya bisa kudurin kwamitin sulhu na MDD da kuma kokarin da bangarori daban daban suka yi.

A game da batun Sham, bangarorin biyu sun bayyana cewa, ya kamata kasashe daban daban su gudanar da kuduri mai lamba 2254, domin daidaita batun ta hanyar siyasa.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China