Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya bayyanawa 'yan jarida cewa, kasashen Sin da Burtaniya na kokarin kafa sabuwar dangantakar kasa da kasa ta yadda kasashen za su zama abokai na hadin gwiwa.
Minista Wang ya bayyana hakan ne a kwanakin baya, a ci gaba da ziyarar aikin da shugaba Xi ke yi a kasar Burtaniya.
Wang Yi ya bayyana cewa, ziyarar shugaba Xi Jinping a kasar Birtaniya ita ce ta farko tun bayan da tsoffin shugabannin kasar Sin suka kai a cikin shekaru 10 da suka gabata, kana ziyara ce mai ma'ana dake shaida cewa, an shiga sabon lokaci na shekaru 10 wajen raya dangantakar dake tsakanin Sin da Birtaniya a dukkan fannoni.
Ya yi imanin cewa, ziyarar ta wannan karo za ta kara inganta dangantakar abokantaka a tsakanin kasashen biyu, da sa kaimi ga kasashen biyu da su kafa sabuwar dangantakar kasa da kasa ta hadin gwiwa da samun moriyar juna.
Wang Yi ya kara da cewa, kamata ya yi Sin da Birtaniya su zama abokan da ke imani da juna. Duk da cewa suna da bambanci a fannonin tsarin kasa, matsayin da ake ciki wajen samun ci gaban al'umma, da kuma al'adu, amma idan suka girmama juna cikin adalci, da kara yin imani da juna a fannin siyasa, za a samu bunkasuwar dangantaka mai dorewa a tsakaninsu.
Bugu da kari, Wang Yi ya ce, ya kamata Sin da Birtaniya su zama abokan da ke samun moriyar juna da bunkasuwa tare. Ya kamata kasashen biyu su kara yin hadin gwiwa a fannonin kirkire-kirkire, samar da kayayyaki, hada-hadar kudi da dai sauransu don kara amfanawa jama'arsu.
Hakazalika, Wang Yi ya ce, Sin da Birtaniya abokai wajen tabbatar da tsaro tare. Kasar Sin tana son ci gaba da yin mu'amala tare da kasar Birtaniya kan batutuwan kasa da kasa da yankuna don sa kaimi ga samun zaman lafiya da kwanciyar hankali a duniya tare. (Zainab)