in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wang Yi: ya kamata a sa kaimi ga aiwatar da yarjejeniyar warware rikicin kasar Sudan ta Kudu
2015-09-30 14:18:31 cri
Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya halarci ganawa a tsakanin ministocin harkokin wajen kasashe biyar mambobin dindindin na kwamitin sulhun MDD da babban sakataren MDD a cibiyar majalissar dake birnin New York na kasar Amurka a ranar talata 29 ga wata.

Game da batun Sudan ta Kudu, Wang Yi ya bayyana cewa, a karkashin kokarin kasa da kasa, bangarorin biyu da rikicin kasar Sudan ta Kudu ya shafa sun daddale yarjejeniyar warware rikicin, an taka muhimmin mataki kan yunkurin shimfida zaman lafiya a kasar, haka kuma an sassauta halin da ake ciki a kasar. Ya ce ana bukatar kara yin kokari wajen aiwatar da yarjejeniyar. Kana kamata ya yi kasashen dake yankin su ci gaba da yin amfani da shiga-tsakani da kungiyar IGAD da kungiyar AU suka yi, kana kwamitin sulhun MDD da kasashe biyar mambobin kwamitin na dindindin su kara yin mu'amala da juna da yin hadin gwiwa, da nuna goyon baya ga kungiyar IGAD da kuma sa kaimi ga shimfida zaman lafiya a kasar Sudan ta Kudu. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China